zazzafar tambaya
Allah jikan Alh. Aminu Dantata! ππππππππ YAN UWA MUSULMI TAMBAYA NAKE YI ## WA YA KE ZATON BA ZASHI LAHIRA BA??? Ta kawar da ARne ta kashe musulmi, Ta tarar da Dan kasuwa da ma manomi, Har da masu tafsirai da masu gurmi, Banda hallakakken dan Adam mujirmi, Wa ya ke tunanin shi ba zai mace ba!? . Ya kamata duk mai hankali ya lura, Ba ta kyale kowa nanya har da yara, Harda masu mulki Wanda ke kujera, Babu Wanda Azra'ilu zaiwa kara, Bashi dakatawa Wanda bai shiri ba. . Babu Wanda zai San lokacin zuwanta, Ko cikin dare ko rana mui jiranta, Wanda ke tunanin sai idan da cuta- Ne ake macewa yaiwa kansa keta, Ban ga Dan Adam mai finsa kuskure ba. . Ko mutum ya so ko karda ma ya yarda, In ta sauka sai ka ganshi yayi banda, Malamai da Kolawa dama Garada, Ta kashe president har maga-takarda, Tunda ta buge Fir'auna bai guje ba. . Ba ta kyale kowa dukkanin halittu, Ta ishe Fakiri mai yawan bukatu, Har Biluniyoyi sun zamo matattu, Da kudi suna sa Dan Adam ya "yantu, Da Ku tabbata Karuna bai mace ba.
Poetry Books 50% Off
Bestselling collections from top poets
