wa kake jira???
wai wa kake jira ya taimake ka? abokanan ka ko kuma ƴan uwan ka? ubangijinka ko iyayen da suka haife ka? amini ko maƙiyin da ke jiran faɗuwarka? indai Allah ne, to shikam ya gama nasa tunda ya baka tunani da hangen nesa yanzu shawara tana ga abinda ka dasa alkhairi ko sharri su zaka ƙyanƙyasa iyayen ka ma sun sauke haƙƙunan su tunda sun baka duk abinda ke garesu na ilimi, tarbiyya dama wanin su kuma sun agaje ka da dukkan ƙarfinsu abakan ka basu da damuwa ko kaɗan idan ka gyaru ka zama cikakken mutun su zauna dakai domin kanada amfanin da suke biɗa a yanzu ko gaba kaɗan su kuwa makiya dama so suke ka faɗi domin su samu batun da zasuyi ta taɗi cikin annushuwa, jin daɗi da zumuɗi rayuwar ka ta kasa cimma mahaɗi.
Poetry Books 50% Off
Bestselling collections from top poets
