faɗima zahra bintu
faɗima zahra bintu, A kanki nake rubutu, Wataran nayi karatu, Da allo nayi ta satu. Idan ba ke ba wace? Kin gaba, kin yi zarce. Son ki ake a dace, Kin wuce ai kwatance. Ƙaunarki nake dagaske, A zance ko a waƙe. Bani batun da bake, Faɗima, dole sai ke.
Ad
Poetry Books 50% Off
Bestselling collections from top poets
Shop Now →
