Barka Da Safiya
Ya ilahi a wagga rana, Na fito da dukan shiri na, Da nufin na yi dangwale na, Don na zaɓi gwani na raina, Wadda zai shiga lammari na, Ya zamo mini shugaba na, Babu ƙarfi kaf guri na, Ko ko wayo mai gudana, Na gareka a kaliqi na, Ban da zaɓi har a rai na, Dukka wadda ka ba shi kai na, Ya zamo mini shugaba na, Za ni bi shi ƙafa da hanna, Na yi roƙo kaliqi na, AlKhairi ya zam gudana, Shugaba mai son lumana, Mun ka roƙo Jalla Rabba.
Ad
Poetry Books 50% Off
Bestselling collections from top poets
Shop Now →
