BAPPAH
To da karfi munka taso, Sako ne munka kunso, Ga mutan birni da kuso, Mu fada musu ba da jinkiri ba. Ban cika ku da baituka na, Bappah kun San jarumi na, In ka so ka kirashi gwamna, Tabbata ba ka yo kure ba. Yan misau naiyo kiranku, Da kare-kare nai batunku, Mun amsa dukan kiranku, Tabbas fa ba ma gaza ba. RESMIDACO manufar mu, Ma'ana ceto kasarmu, Daga hannun laisa ilmu, Marasa manufa ku duba.
Ad
Poetry Books 50% Off
Bestselling collections from top poets
Shop Now →
